Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Na Tababar Ganawarsa Da Shugaban Koriya ta Arewa


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Duk da karfin gwuiwar da sakataren harkokin wajen Amurka ke dashi na cewa Trump da Kim Jung Un zasu yi taron kolinsu kamar yadda aka shirya, shugaban Amurka Donald Trump ya soma shakkar taron zai gudana

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce mai yiwuwa ganawar da aka shirya yi tsakaninsa da Shugaban Koriya Ta Arewa a watan gobe, ba za ta tabbata ba.

“Idan ba a yi ba, watakila za a yi nan gaba,” a cewar Trump. Ya kara da cewa, “Mai yiwuwa ba za a iya yi a ranar 12 ga watan Yuni ba.”

Da ya ke magana a fadarsa da Shugaban, Koriya ta Kudu Moon Jae-in, Trump ya ce, “Akwai wasu yanayi da mu ke son gani. Ina jin za mu samu wadannan yanayin.”

Da aka tambaye shi irin yanayin da yake nufi, sai Trump ya ce, “Bai kamata na fada ba.” To amma batun kawar da makamin nukiliya a Koriya ta Arewa “Dole ya faru.”

Shi ma da ya ke bayani a taron manema labarai da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta kira, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo, ya ce har yanzu Amurka na shirye-shiryen ganawar a ranar 12 ga watan Yuni, to amma bai tabbatar ko ganawar za ta yiwu ba. To amma ya ce ya na da karfin gwuiwar cewa karshenta dai za a kai ga ganawar.

Facebook Forum

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG