Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya fidda wasu jerin bukatu akan cimma yarjejeniyar makaman nukiliya da Iran, ya kuma yi barazanar sanya tsauraran takunkumi masu karya tattalin arziki idan har Iran ba ta canza dabi’un ta ba. Wannan sabon gargadin na zuwa ne a wani jawabi da ya bayyana tsarin gwamnatin Trump biyo bayan matakin da Amurka ta dauka na fita daga yarjejeniyar makaman nukiliya.
"Tabbas wannan zai kasance takunkumi mai tsanani da aka taba sanyawa a tarihi idan muka kammala, bayan takunkumin mu ya fara aiki, Iran zata ji jiki wajen kokarin ceto tattalin arzikin ta.''
Jawabin Pompeo na zaman wani yunkuri na fidda manufofin Amurka na cigaba bayan da shugaba Donald Trump ya fidda kasar daga yarjejeniyar makaman Nukiliyar Iran a farkon watan nan.
A makon da ya gabata kungiyar tarayyar Turai ta fara wani shiri wanda zai kare kamfanonin kasashen Turai da za su so su yi kasuwanci a Iran.
Facebook Forum