Hakan ya faru ne da nufin maida martani ga munanan kalaman da ministan harakokin wajen Faransa Jean Yves le Drian ya furta akan mahukuntan Malakan
Tun a washe garin juyin mulkin da ya kifar da Ibrahim Boubacar Keita daga karagar mulki ne aka fara samun tsamin dangantka a tsakanin Mali da Faransa lamarin da ya kara kwabewa bayan da Kanar Assimi Goita ya yi wani juyin mulki na 2 a kasar da ta shafe shekaru da dama cikin halin tabarbarewar tsaro.
Dadin dadawa abubuwa sun kara lalacewa bayan bayyanar labarin shirin girke sojan Russia a Mali. A na cikin wannan yanayi ne Ministan harkokin wajen Faransa Jean Yves le Drian ya caccaki gwamnatin rikon kwaryar Mali wacce ya ayyana a matsayin marasa kima da dattako mafarin korar jakada Joel Meyer.
To amma Moustapha Abdoulaye na wata cibiyar nazari da bincike akan sha’anin tsaro na mai jan hankulan kasashen 2 game da rashin dacewar takaddamar diflomasiyar da ta kunno kai a tsakaninsu a yayinda ake faman neman hanyoyin murkushe ayyukan ‘yan ta’adda a yankin sahel.
Kafin ta kori jakadan Faransa daga Bamako gwamnatin Mali a makon jiya ta kori sojojin Denmark kimanin 100 saboda a cewarta an shigo da su kasar da sunan yaki da ta’addanci ba da izininta ba.
Tuni matakin korar jakadan Faransar daga Mali ya fara daukan hankulan ‘yan takarar dake kalubalantar shugaba Emmanuel Macron a zaben dake tafe wadanda dama ke kushe matakin girke dubban sojojin Barkhane a Yankin Sahel.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5