A makon jiya rahotanni suka nuna cewa ana kokarin sake jadawalin zaben da tun farko akace za a gudanar a watan Yuli, haka kuwa ya fito fili ne bayan wata ziyarar ba zata da gwamnan jihar Sanata Muhammadu Umaru Jibrilla Bindo ya kai a majalisar dokokin jihar. inda yace wannan ziyarar sada zumunci ce, sai dai da alamu ‘yan majalisun basu goyi bayan maganar ba.
Itama jam’iyyar APC dake mulkin jihar wadda kawo yanzu ma tayi rijistar ‘yan takarar shugabancin kananan hukumomi fiye da 100 baya ga na Kansiloli tace ba zata sabuba. Sakataren tsare tsaren jam’iyyar Alhaji Ahmed Lawal, yace maganar bayar da riko ma baya cikin doka kuma jam’iyyar APC bazatayi abinda baya cikin doka ba.
A bangaren gwamnatin jihar kuwa Hon Ahmed Sajo, mai zama kwamishinan yada labaran jihar yayi bayanin cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta jiha ita ce ke tsara jadawalinta, to amma idan har ma’aikatan gwamnati zasu ci gaba da saka hannu kan harkar siyasa to hakan zai iya lalata kwarewarsu a aiki, ya kuma ce ba laifi bane a samu wasu da zasu shugabanci kananan hukumomi na dan wani lokaci, kuma basa son ma’aikatan gwamnati su tsoma hannu kan harkar siyasa.
Yanzu haka dai lokaci ne kadai zai iya tabbatar da cewa ko za a sauya lokacin zaben ko ba haka ba.
Saurari rahotan.
Your browser doesn’t support HTML5