SIYASAR AMURKA: Yakin Nemar Zabe
Ana cigaba da fafatawa a yakin nemar zaben Shugaban kasar Amurka. Ga bayanin da abokin aikinmu Ibrahim Jarmai ya fassara:
“Yanzu haka, dan takarar shugabancin Amurka a karkashin jam’iyar Republican, Donald Trump, ya fi maida hankalinsa ne kan tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, Hillary Clinton, bayan da ‘yan takarar biyu suka lashe zabukan fidda gwani da da aka yi a jihar New York.
A ranar Larabar da ta gabata Trump ya yi wani gangamin yakin neman zabensa a Jihar Maryland, daya daga jahohi biyar da za a yi zabe a ranar Talata mai zuwa.
Sai dai duk wadannan kalamai na Trump, ya na bukatar da farko jam’iyarsa ta tsaida shi tukuna, kuma mutunan da su ke kara nisanta shi da hakan su ne Sanata Ted Cruz na Texas da gwamnan Ohio, John Kasick, wadanda dukkaninsu ke biye da shi, a yawan wakilai, kuma su ke so su zama karfen kafa a burinsa na mallake tikitin jam’iyar a watan Yuli mai zuwa.
A daya bangaren kuwa, Hillary Clinton ta yi nata gangamin yakin neman zaben a Pennsylvania a ranar Larabar da ta gabata, inda ta guji ambatar sunan Trump a lokacin da ta ke jawabi, sai dai ta caccaki abokin hamayyarsa a jam’iyar ta Republican, wato Ted Cruz, wanda shima ya dauki wata matsaya makamanciyar ta Trump.”
Ga dai Ibrahim Jarmai da cikakken bayanin: