Kisan Mutane 17, "Hukumar Bincike Ta FBI Ta Sha'afa," Inji Trump

  • Ibrahim Garba

Shugaban Hukumar FBI, Christopher Wray.

A cigaba da faruwar sa'insa tsakanin Shugaban Amurka Donald Trump da Hukumar Bincike ta FBI, Shugaba Trump ya zargi hukumar da sha'afa wajen kokarin tabbatar da zargin cewa Rasha ta maikama masa a zaben 2016.

Shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki babbar hukumar tabbatar da bin doka da oda ta Amurka (FBI), saboda abinda ya kira, “rashin mai da hankali kan alamomin da su ka bayyana” tun kafin wani matashi dan shekaru 19 da haihuwa ya je ya yi harbin kan mai uwa da wabi a wata makarantar Sakandare a Florida a makon jiya.

Trump ya ce, “Abin bakin ciki hukumar bincike ta FBI ta kasa mai da hankali kan alamomi da dama da su ka bayyana daga maharin nan na makarantar Florida. Ba za mu yadda da haka ba.” Abin da Trump ya rubuta Kenan ta kafar twitter jiya Asabar. Ya kara da cewa, “Jami’FBI sun bata lokaci mai yawa wurin kokarin tabbatar da zargin cewa Rasha ta hada baki da Kwamitin Yakin Neman Zaben Trump – alhalin kuwa babu wani hadin bakin da aka yi. Ku koma bakin aikin da ya wajaba gare ku don a yi alfahari da ku!” in ji Trump.

Ranar Jumma’a hukumar bincike ta FBI ta amsa cewa lallai ta kasa amfani bayanan da aka rada ma ta game da maharin kafin ya je ya hallaka mutane 17.