Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tuhumi 'Yan Kasar Rasha 13 Da Kamfanoni 3 Da Katsalandan A Zaben Amurka


Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump

Kwamiti na musamman dake bincike katsalandan da ake zargin Rasha da yi a zaben shekara ta dubu biyu da goma sha shida ya tuhumi Rukunin Rashawa na farko da ake zargin suna da hannu a wannan yunkurin. Rukunin ya kunshi 'yan kasar Rasha goma sha uku da kuma wadansu kamfanonin Rasha uku

A cikin takardar tuhumar da masu taimakawa gwamnatin tarayya tantance laifi suka bayar, an yi zargin cewa, wani kamfanin nazarin hanyar sadarwar internet dake da cibiya a Rasha, wanda kuma yake da alaka da Kremlin, da ma'aikatansa goma sha biyu sun gudanar da wadansu ayyuka da nufin yin katsalandan a zabe, da kuma tsarin siyasar Amurka daga shekara ta dubu da dari biyu da goma sha hudu zuwa zaben shugaban kasa na shekara ta dubu biyu da goma sha shida.

An hakikanta cewa, kamfanin ya taka muhimmiyar rawa a katsalandan din da ake zargin Rasha da shi a zaben shugaban kasa, ta wajen yin aiki da shafunan sadarwa na boge, da biyan masu amfani da hanyar sadarwar internet da wadansu hanyoyi da nufin karkata sakamakon zaben don shugaba Donald Trump ya sami galaba.

An kuma tuhumi mai daukar nauyin cibiyar nazarin ta hanyar internet, wani dan kasuwar kasar Rasha Yevgeniy Prigozhin, da wadansu kamfanoni biyu dake karkashin ikonsa,Concord Management da Consulting and Concord Catering. Takardar tuhumar ta bayyana cewa, Prigozhin da cibiyoyin kasuwancinsa. sun bada makudan kudi ga kamfanin nazarin hanyar sadarwar internet da nufin yin katsalandan a zaben da aka gudanar a Amurka cikin shekara ta dubu biyu da goma sha shida.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG