Rahotanni daga sassa daban daban na birnin Legas dai sun tabbatar da cewar babu tashin hankali a inda suke. Sai dai a yayinda ake cikin zaman wannan yanayi suma al'umman Hausawa da Fulanin da malaman addinin musulunci naci gaba da jan hankalin makiyaya da su guji shiga harkokin ta'addanci, a maimakon haka su kasance masu bin doka da oda domin zaman lafiyan Najeriya baki daya.
Wasu yan arewancin Najeriya da Muryar Amurka ta tuntunba suna cewa ya kamata su fulanin makiyaya ko su yi wa 'yan'uwansu magana ko su kalubalance su, don su daina aikata ta'addancin, kuma da su dakatar da aikin ta'asan da su ke yi.
Sun bayyana cewa sama da kashi casa'in cikin dari na masu garkuwa da mutane Fulani ne, kuma wannan ba abu ne da duk mai kaunar zaman lafiya zai lamunta ba,
Yanzu dai jama'a na jiran ganin matakan da gwamnati zata dauka na dawo da doka da oda a sassan kasar, da kuma fatar ganin an samu kwanciyan hankali da lumana a kasar.
Saurari cikakken rahoton a cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5