Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya yiwa jama’ar, da ruwan sama da iska ya yiwa barna a garin Kuta alkawarin tallafi da Gwamnatin jihar.
Yayi wannan alkawarin ne a lokaci da ya ziyarci garin na Kuta, a karamar hukumar Shiroro, domin jajantawa mutanen.
Kimanin mutane dubu daya ne suka rasa muhallansu a sanadiyar wannan mummunar guguwar a garin na Kuta.
Duk da yake dai ba’a samu hasaran rayuka ba amma lamarin ya jefa dinbin jama’a cikin damuwa a sakamakon hasarar dukiya.
Malam Umar Garba, Dan Madamin Kuta, ya kira ga hukumomin da hakkin ya rataya a wuyansu dasu gaggauta taimakawa jama’ar gari domin ceto su daga cikin wannan mummunar yanayin da suka samu kansu a cikin sanadiyar wannan guguwar.
Dan Majalisar wakilan Najeriya, Chika Adamu, da ya kai ziyarar jaje ya bada gudumawar Naira miliyan daya, tare da yi masu nasiha cewa sun maida alamarin ga Allah.
Yana mai cewa” Wannan abu yazo a daida lokacin da mutane ke hannu baka hannu kwarya, amma idan duk muka maida ga Allah, toh tabbaci hakika Allah zai mana maganin abun,masifu suna zuwa a matsayin jarabawa domin mu duba baya, kuma wanda bata sameshi bat oh ya tausayawa wanda ta sameshi, saboda idan ka tausayawa wanda musifa ta afkawa kaima Allah zai kara tausaya maka kuma zai kara kare ka.”