A wani taron karawa juna sani da hukumar Kustan reshen jihar Lagos, da kuma masu ruwa da tsaki wajen kiwon kaji da lafiya, ta gudanar a Lagos.
Sun bayyana bukatar mutane su kiyaye wajen cin kajin da ake shigowa dasu daga kasashen waje wadanda aka riga aka sarrafa.
A cewar babban mai kula da hukumar ta kwastan, reshen jihar Lagos Alhaji Turaki Usman hukumar ta dukufa wajen hana shigowa da kajin da aka sarrafasu daga kasashen kitare abisa shawaran jami’an kiwon lafiya.
Kungiyar masu kiwon kaji ta kasa ta koka game da rashin biyan cikakken diya ga ‘yayan kungiyar da aka rufe gonakinsu a can baya sabili da kamuwa da cutar muran tsuntsaye da akasari kajin kasar sukayi.
Sakataren kungiyar ta kasa Alhaji Baba Gana, yace idan dai Gwamnati bata dauki wani mataki na biyan diya ba to ko shakka babu matakan da take so ta dauka na ganin an kyautata kiwon kaji a cikin gida yana cike da matsaloli da dama.
Yanzu dai babban gargadi da hukumomin lafiya keyi na cin kajin da ake shigowa dasu daga kasashen waje bayan an sarrafasu shine na kamuwa da cutar Cancer wato Sankara ko Daji, a sabili da sinadarai da ake saka masu domin hanasu lalacewa da wuri.