Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karin Magana Mai Kambamawa


Dr. Abdullahi Garba Imam
Dr. Abdullahi Garba Imam

A shirin Harshe Da Karin Magana har yanzu muna tare da Dakta Abdullahi Garba Imam, na kwalejin Mallam Aminu Kano.

Dakta Abdullahi ya bayyana yadda karin magana mai kambamawa, shi wannan karin magana shine wanda za’a fadi wata magana to mutane sun san cewa wannan abun fa bai taba faruwa ba, to shine sai bahaushe ya ‘dauko irin su ya tayar da karin magana wanda ake kiransa mai kambamawa.

Kuma shine karin magana mai kunshe da lafazozi masu wuyar afkuwa, koma bazasu afkuba gaba daya, amma sai ace sun afku. Missalin daya daga cikin ire-iren wadannan karin maganar shine “Abun mamaki Kare da tallar tsire” to anan anzo da abinda bazai yiwu ba, domin kadaurawa kare tallar tsire tabbas cinyewa zai yi.

Saurari hirar Dakta Abdullahi da wakiliyar Dandali Baraka Bashir.

XS
SM
MD
LG