Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hidimomin Sallah da Bashi


Hidimar Sallah
Hidimar Sallah

Bisaga al’ada duk lokacin da yarage kwanaki kadan zuwa ga salla karama, jama’a kanyi tururuwa zuwa kasuwanni da shaguna, domin sayan kayan sallah ga ‘yayansu dama mata. A wannan shekarar abun bai chanza ba dai, donkuwa filin Dandalin VOA yayi zagaye cikin wadannan kasuwanni, inda mukayi karo da wasu mata dasuke koakarin sayan kayan sallah ma kansu da ‘yayansu.

A wani shago dai da muka ga mata sunyi tururuwa, muntattauna dasu wanda suka bayyanar da irin shirye shiryen da sukeyi, sukanzo wannan shago a duk shekara domin kuwa mai wannan shagon, yakan saida musu da kaya cikin rahusa. Sukan siya takalma, gyale, huluna, da dai makamantan hakan.

A tabakin mai wannan shagon, sukan rage kayansu a duk lokaci irin wannan, saboda hakan nada matukar mahimanci, ganin wannan watane mai falala. Suna kokari suyi koyi da koyarwar Manzon rahama da yayi nuni da a saukakama masu karamin karfi a wannan watan, kuma a kasashen duniya ma, akan rage kudaden kaya don kyautatama al’uma. Don haka yasa sukarage kimanin kashi ashirin zuwa talatin a wannan lokaci.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG