Francis ya yi tsokaci ne yayin da yake nada wani Bishop na karni na 19 da aka fi sani da "uban bakin haure" da kuma wani mutum wanda ya yi wa marasa lafiya hidima a Argentina.
Francis wanda ya nuna goyon bayansa ga bakin haure a matsayin babban jigon fadar sa, ya jagoranci bikin a gaban mutane 50,000 a dandalin St. Peter.
Da yake jawabi a wajen bukin, Paparoman ya bayyana cewa, "Kebe bakin haure abin kunya ne, haƙiƙa, keɓe bakin haure laifi ne, wannan zai sa su mutu a gabanmu."
“Don haka a yau tekun Bahar Rum shi ne makabarta mafi girma a duniya,” in ji shi, yayin da yake magana kan dubban da suka nutse a kokarin shiga Turai.
Ana sa ran Giorgia Meloni za ta zama firayim minista a karshen wannan watan na shugaban gamayyar kungiyoyin da suka sha alwashin murkushe bakin haure tare da tsaurara iyakokin Italiya.
Ta yi alkawarin hanzarta komawa gidan bakin haure da kuma tsauraran dokokin na neman mafaka. Meloni ta kuma yi kira da a killace jiragen ruwa na arewacin Afirka domin hana bakin haure yin tafiya tare da sabunta matakan dakile jiragen ruwan agaji.
Francis, wanda bai ambaci Italiya ba, ya ce wasu bakin hauren da akan maido da su ana sanya su a “sansanoni masu tada hankali inda ake cin gajiyar su da kuma rike su a matsayin bayi.” A baya ya ce hakan ya faru a kasar Libya.