A mako mai zuwa an shirya Fafaroma Francis zai ziyarci kasar Chile da Peru, ziyarar da aka tsara saboda mayar da hankali kan matsalolin ‘yan asalin kasashen, amma da alamu batun abin fallasa na lalata a coci da rikicin siyasa a kasar Peru, zasu dabaibaye ziyarar.
Kwanaki kadan kafin wannan ziyara, wasu ‘yan tayar da zaune tsaye suka kaiwa Majami’u uku hari a babban birnin Santiago na Chile, suka kuma bar wani rubutaccen sako dake cewa: “Fafaroma Francis, bam na gaba zai tarwatsaka.”
A jiya Juma’a ne jami’ai sukace babu wani da ya sami ko rauni a hare-haren da aka kai, in banda ‘yan kananan barna da aka yi.
Shuabar kasa Michelle Bachelet ta yi kira ga ‘yan kasar Chile da su karbi Fafaroma cikin mutunci, ta kuma ce har yanzu ba a san ko su waye suka shirya harin ba.
Facebook Forum