Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fafaroma Francis Yayi Kiran Hakuri Da Yafewa Juna A Columbia


Mai Alfarma Fafaroma Francis
Mai Alfarma Fafaroma Francis

Mai alfarma Fafaroma Francis na cigaba da ziyara a Columbia

Mai Alfarma Fafaroma Francis ya yi kira ga Al’ummar Columbia da suyi watsi da ramuwar gayya, a yayin da suke ci gaba da kokarin kawo karshen yakin basasar da aka kwashe shekaru fiye da 50 a nayi a kasar.

Yayin da Fafaroma Francis ke gudanar da taron addu’a da mutane masu dinbin yawa a wani fili dake Bagota, yayi kira ga shuwagabannin Colombia da su kafa dokar da zata kawo karshen nuna banbanci wanda ke haifar da tashe tashen hankula.

Kawunan 'Yan Colombia sun rarrabu matuka ya yin da suke shirin karbar dubban tsoffin mayakan kungiyar sunkuru ta FARC a cikin al’umma gami da gyara rabe-raben da ke tsakanin su bayan yakin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 220,000 cikin fiye da shekaru 50.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG