Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fafaroma Francis Bai Ambaci Rikicin Rohingya Ba A Jawabinsa A Myanmar


Kusan mutane 150, 000 ‘yan Cocin Katolika a fadin Myanmar suka hadu a filin wasannin Kyaikkasan don taron sujadar, wasu tun da dare suka isa don su sami wurin zama.

A wajen wani taron sujadar da dubban ‘yan Myanmar suka hallarta a birnin Yongon, birni mafi girma a Myanmar, yau Laraba Fafaroma Francis yayi magana akan bukatar yin gafara da kuma kaucewa yin ramuwar gayya.

Sai dai karo na biyu ke nan kai tsaye bai ambaci batun kisa da kuntatawar da aka yiwa musulmin Rohingya ba a ziyarar da yake yi ta kwanaki 4 a kasar, bayan da yayi jawabi akan mutunta addinin wasu a wata ganawa da yayi da jami’an diplomasiyya jiya Talata.

Fafaroma, wanda ke yawan jan hankali akan a taimakawa ‘yan gudun hijira, ya ba mutane dayawa daga kasashen yammacin duniya mamaki, wadanda suka yi hasashen zai yi magana akan rikicin Rohingya a bainar jama’a.

‘Yan Rohingya fiye da 620,000, tsirarun musulmin da aka dade ana kuntatawa ne suka tsere daga kasar zuwa Bangladesh tun daga watan Agusta bayan wani farmaki da sojojin kasar suka kai masu.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG