Shugaban hukumar alhazan Najeriya Barrister Abdullahi Mukhtar Muhammad ya bayyana adadin alhazai 56 da suka rasa rayukansu a sakamakon turmutsitsin tafiya jifar Shaidan a Mina.
Alhazai 42 suka rasu daga jihohi. Biyu daga hukumar alhazai ta kasa sai kuma goma sha biyu daga kamfanonin jiragen yawo.
Shugaban hukumar yace an kafa kwamitoci karin bincike, ta'aziya da shirin jana'izar marigayin.
Jakadojin Najeriya dake Riyadh da Jidda sun kasance a wurin bisa ga umurnin shugaban kasa Muhammad Buhari saboda su yi aki tare da kuma karfafa masu gwiwa.
Har wa yau akwai gawarwakin da kawo yanzu ba'a tantancesu ba. Likitan alhazai Dr Ibrahim Kana yace za'a yi anfani da dabarun likita wajen ganosu.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5