An nuna hotun bidiyon gawarwakin mutane a kasa, da wadanda suka ji raunuka wadansu kuma suna kuka a Minna dake tazarar kilomita biyar da birnin Makka.
Mahajjata suna zuwa wurin ne domin jifar shaidan, aikin ibada na karshe kafin bukin sallah.
An yi jerin gwano ana fuskantar zuwa wuri guda ne da rana, kafin wani rukunin mahajjata ya juya ya fara komawa, abinda yasa aka rika karo ana tattake mutane maza da mata, tsofaffi da majiya karfi.
Wakilin Sashen Hausa Nasiru Adamu El-Hikaya ya bada rahoto cewa, turmutsutsun ya faru ne a wurin ayyukan ibada dake Mina, inda aka kafa sama da tantuna dubu dari da sittin domin masu aikin hajji.
Wannan turmutsutsun shine sanadin asarar rayuka na biyu da aka samu wannan watan, bayan gocewar wata kugiyar daukar kayan gine gine da tayi sanadin mutuwar mutane dari da tara a birnin Makka bana.