Jiya Asabar aka kammala aikin Hajji na bana ba tareda wata sabuwar matsala ba, a yayinda adadin wadand suka halaka a turereniyar ya haura zuwa 769.
Ministan kiwon lafiya na Saudiyya Khalid al-Falih ya fada jiya Asabar cewa, mutane 934 ne suka sami raunuka sakamakon hatsaniyar data auku a Muna, dake bayan garin Makka. Mahajjatan kasar Iran su 136 ne suka rasa rayukansu.
Tashar talabijin ta kasar tace tsohon jakadanta a Lebanon, yana daga cikin fiye da mahajjatanta 300 da har yanzu ba'a san inda suke ba.
Iran tana zargin kasar Saudiyya da laifi, da kuma nuna gazawa, daga nan ta lashi takobin sai ta gurfanar da ita a gaban kotun kasa da kasa. Shugabannin Iran suka ce masarautar saudiyya ba zata iya daukar nauyin shirya aikin Hajji inda mutane sama da milyan biyu suke haduwa ba.
Ahalinda ake ciki kuma, hukumar aikin Hajji ta jihar Taraba dake arewa maso gabsshin Najeriya ta tabbatar da mutuwar Amirul Hajji daga jihar, wanda kuma sarki ne mai daraja ta daya, na masarautar Zing Alhaji Abbas Sambo. Anyi jana'izarsa ranar Jumma'a a Saudiyya. Ga Ibrahim Abdulaziz da ci gaban rahoton.