Yanzu dai jami'an hukumar alhazai suna cigaba da daukan sunayen alhazansu domin tantancesu da gano adadin wadanda suka rasa rayukansu ko suka samu rauni.
Jami'an alhazan daga kasashe daban daban sun hada da zagayawa asibitoci domin ko zasu gano nasu yayinda mahukuntar kasar ta Saudiya suka tabbatar da mutuwar alhazai 717.
Yau tun daga asubahi jirage masu saukar angulu suke zagayawa da zummar gano karin gawarwaki da watakila basu gani ba jiya lokacin da lamarin ya auku.
Kazalika an kafa kwamitin bincike a san musabbabin aukuwar turmutsitsin da kuma kiyaye na gaba.
Kawo yanzu hukumar alhazan Najeriya bata fitarda sunayen wadanda suka rasu ba sai wani lokaci yau amma babu shakka sunayen Farfasa Tijjani El-Miskin da Bilkisu Yusuf na cikin wadanda aka ce sun rasa rayukansu. Wasu alkalumma kuma sun nuna cewa 'yan Najeriya kusan talatin ne suka rasu sanadiyar turmutsitsin.
Kodayake Jakadan Najeriya dake Saudiya ya tabbatar da aukuwar lamarin amma ya ki ya fadi adadin 'yan Najeriya da suka rasu. Yace har yanzu ana kokarin tantancewa. Sai hukumomin Saudiya sun sanarda su kana zasu sanarda hukumomin Najeriya.
Ma'aikatar harkokin kasashen wajen Najeriya da ofishin shugaban kasa sun kira Jakadan Najeriya domn samun bayani da bada shawara. Jakadan ya gargadi alhazai kada su dinga fitowa lokaci guda zuwa jifan Shaidan saboda ana zafi matuka.
Ga karin bayani.