Buhari ya bayyana hakan ne a wata rubutacciyar sanarwa da ya fitar dauke da sa hanun mai bashi shawara kan hulda da ‘yan jarida , Malam Garba Shehu.
A cewar shugaban na Najeriya, wannan bala’i da ya kai mutuwar fitacciyar yar jaridar nan Hajiya Bilkisu Yusuf da Farfesa Tijjani El-Miskin da sauransu abin alhini ne ga daukacin al’uman musulmin duniya.
Shugaban ya kuma mika ta’aziyyarsa gag a iyalan sama da mutane 700 da suka rasu a wannan bala’i da ya faru kasa da makwannin biyu da wanda ya halaka mutane da dama a Makka.
Sanarwar ta nuna cewa shugaba Buhari ya yi na’am da alwashin da hukumomin Saudiya suka sha na cewa za su binciki wannan lamari.
Ya kuma yi kira ga Sarki Salman da ya ga cewa an gano kurakuran da ke tattare da aikin hajji domin kaucewa aukuwar irin wannan lamari.