Fannin Noma A Ghana Na Fuskantar Barazana Saboda Kaurar Jama'a Daga Kauyuka Zuwa Birane

Manoma

Rahoton baya-bayan nan da hukumar NDPC mai fafutukan samar da ci gaba ta kasar ta fitar, na cewa, tsakanin shekarar 2017 zuwa 2022, an samu karin fiye da kashi sittin cikin dari na mazauna yankuna karkara da ke kaura daga arewa mai nisa zuwa cikin birane.

ACCRA, GHANA - A jihohin arewa mai nisa a kasar Ghana, an fi amfani da matasa wajen noma amma kuma mafi yawancin matasa na sauya matsuguni zuwa birane, abin da ke barazana ga samar da isashen abinci.

Mallam Aminu Champagn shugaban mazauna a matsugunin masu kwararowa daga jihohin arewa dake Kumasi ya bayyana cewa ko shakka babu sana'arsu ita ce noma amma rashin inganta ayyukan noma ne ya kaisu ga sauya matsuguni zuwa birane.

Mai sharhi bisa harkar noma ta kasa Mallam Jafaru Dankwabiya ya jaddada muhimmancin daukan mataki ko kuma Ghana ta tsunduma cikin halin rashin isashen abinci saboda rashin manoma ajihohin arewa da akafi noma a kasar na rage yawan abinci da ake shukawa saboda babu ma'aikata.

Mallam Saalim Bamba jami'i a hukumar raya ci gaban tsakiyar birane da zangwanni fadin kasar Ghana ya ce gwamnati ta inganta wasu shirye-shirye domin taimakon manoma, ciki harda tallafin shuka domin samar da sana'a da abinci da dai sauransu.

Ya kuma kara da cewa gwamnati zata ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin shawo kan matsalar kwararan al’umman arewa zuwa birane.

Jihohin arewa mai nisa suke kan gaba wajen noman abinci wanda jama'arsu zasu ci tare da fitarwa zuwa birane da ma kasashen waje domin samarma kasar kudaden shiga.