Gwamnatin Ghana ta tabbatar tare da ware ranar Asabar ta biyu a kowane wata a matsayin ranar motsa jiki ta kasa.
Manufar tabbatar da wannan rana ita ce, wayar da kan jama'a game da fa'idoji da yawan motsa jiki, tare da karfafawa 'yan Ghana kwarin gwiwa a kan su rike dabi'ar motsa jiki don kare kai daga wasu cututtuka.
Daga cikin manyan jami’u da manyan baki da suka halarci karon farko na motsa jikin, sun hada da ministan wasanni, Hon. Mustapha Ussif, da sarkin Ankarawa, Ga Mantse Nii Takie Teiko II, da ministoci da shugaban hukumar kwallon kafa ta Ghana, Kurt Okraku, da shugaban kwamitin Olympic na kasa, Ben Noonu-Mensah da tsohon zakaran damben duniya na WBC, Azumah Nelson da sauransu.
Bayan an yi tattaki zuwa wasu manyan titunan birnin Accra sai aka garzayo zuwa babban filin wasanni na kasa. A gajeren jawabi da mataimakin shugaban kasa, Dakta Mahamudu Bawumia ya yi a wajen taron, ya shawarci jama’a da su yi amfani da irin wannan rana domin inganta lafiyarsu. Ya ce, a lokacin da aka bayyana kudurin ranar motsa jiki ta kasa a majalisar zartarwa, shugaban kasa Nana Akufo-Addo ne na farko da ya amince.
Dakta Bawumia, ya kara da cewa, ana so a tabbatar da cewa Ghana ta na cikin koshin lafiya, kuma ranar motsa jiki ta kasa za ta taimaka wajen inganta lafiyar al’umma, kuma a zahiri hakan na nufin samar da ci gaba a kasar.
A nasa bangaren ministan matasa da wasanni ya nuna matukar godiyarsa ga duk wadanda suka taimaka aka samu gagarumar nasara ga wannan manufa. Kuma ya sake nanata cewa, shirin ranar motsa jiki ta kasa ya zo ya tabbata ne, a duk ranar Asabar ta biyu na kowane wata. Kuma za a din ga zagayawa duk yankunan kasar.
Wasu mahalarta taron sun bayyana ra’ayinsu a kan muhimmancin kirkirar irin wannan rana domin motsa jiki. Suka ce, lallai hakan na kyau domin za samu Karin lafiyar jiki da walwala.
Saurari rahotan Idris Abdullah Bako: