Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matakan Da Ghana Ta Bi Wajen Samar Da Daidaito a Tsakanin Jinsi A Fannonin Ilimi, Lafiya - Dr. Bawumia


Mataimakin shugaban kasra Ghana, Mahamudu Bawumia yayin wata ziyara da ya kawo Washington D.C. a watan Afrilun 2017
Mataimakin shugaban kasra Ghana, Mahamudu Bawumia yayin wata ziyara da ya kawo Washington D.C. a watan Afrilun 2017

Sai dai masu fashin baki da manazarta a Ghana, na nuni da cewa har yanzu da rina a kaba, domin akwai bangarori da yake bukatar kulawa a daidaiton jinsi, musamman yawan mata a majalisar dokokin kasar; yawan ministoci da shugabanin birane da gundumomin kasar.

Mataimakin shugaban kasar Ghana, Dakta Mahamudu Bawumia, ya bayyana wasu ingantattun manufofi da gwamnatinsu ta aiwatar kuma suka taimaka wajen samar da karin daidaiton jinsi a Ghana, musamman a bangarorin ilimi, lafiya da tattalin arziki.

Ya bayyana hakan ne a taron kasuwanci, zuba hannun jari da ci gaba tsakanin Afirka da Karibiya na farko, wanda aka gudanar a kasar Barbados.

Magance rashin daidaito tsakanin jinsi, na daya daga cikin batutuwan da aka yi magana a kai a yayin wani zaman tattaunawa na taron.

Da yake amsa tambaya kan yadda gwamnatinsa ke kokarin dakile matsalar, Dakta Mahamudu Bawumia ya zayyana wasu tsare-tsare da suka shirya da nufin cike gibin da yake tsakanin maza da mata a fannonin rayuwa da dama.

A bangaren ilimi, mataimakin shugaban kasar ya ce, bincike ya nuna cewa mata sun fi yawan fita daga makaranta kafin su kammala fiye da maza.

Tsarin Ilimin sakandare kyauta ya sa wadanda a da ba su iya yin rijista domin rashin kudi, yanzu suna yi, kuma mata sun fi yawa.

Ga bangaren kiwon lafiya da tattalin arziki kuwa, mataimakin shugaban kasar ya ce saboda yawancin mata na da wayoyin hannu, sai suka gabatar da hadin gwiwar asusun wayar hannu da asusun banki, wanda hakan ya sa yawancin su yanzu sun mallaki asusun banki.

Haka kuma gwamnati ta fito da tsarin aikawa da magunguna zuwa kauyuka ta hanyar jirgi mara matuki, kwalliya tana biyan kudin sabulu, musamman ga mata masu nakuda domin ana aikawa da jini a wadannan jiragen kuma yana ceto rayukan iyaye da jinjiran da ake haihuwa a kauyukan da babu asibiti kusa.

Sai dai masu fashin baki da manazarta a Ghana kamar Malam Mairago Jibril Abbas da Abubakar Garba Osman na nuni da cewa har yanzu da rina a kaba, domin akwai bangarori da yake bukatar kulawa a daidaiton jinsi, musamman yawan mata a majalisar dokokin kasar; yawan ministoci da shugabanin birane da gundumomin kasar.

Kididdigar da kungiyar Tattalin Arziki ta Duniya ke fitarwa duk shekara a kan gibin da ake samu tsakanin jinsi na kasashen duniya na shekarar 2021 na cewa; kasar Ghana na da jimillar kaso 66.6 cikin 100; a bangaren ikon a siyasa kuwa, Ghana na da kaso 13.5 kacal cikin 100.

Saurari cikakken rahoton Idris Abdullah:

Matakan Da Ghana Ta Bi Wajen Samar Da Daidaito a Tsakanin Jinsi A Fannonin Ilimi, Lafiya - 3'48" .MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:48 0:00

XS
SM
MD
LG