Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Ta Gurfanar Da Wasu ‘Yan China Kan Laifukan Hakar Ma’adanai Ba Bisa Ka'ida Ba


Gwamnatin Ghana Ta Gurfanar Da Wasu ‘Yan China Akan Laifukan Hakar Ma’adanai
Gwamnatin Ghana Ta Gurfanar Da Wasu ‘Yan China Akan Laifukan Hakar Ma’adanai

Gwamnatin Ghana ta gurfanar da wasu 'yan kasar China su hudu ciki harda shahararriyar mai hakar ma'adinai a Ghana, Huang Ruixia, da aka fi sani da Aisha Huang, a gaban babban kotun Accra.

KUMASI, GHANA - Alkalin kotun ya tasa keyarsu zuwa wurin ci gaba da jiran shari'a ko "remand" bisa laifukan hakar ma'adinai ba bisa ka’ida ba tare da aikata wasu abubuwan da suka saba wa dokar kasar, awani matakin kawar da matsalar hakar ma'adinai ta barauniyar hanya da gwamnatin kasar ta dauka.

Sai dai ba wannan ne matakin farko da gwamnati ta dauka wajen magance matsalar hakar ma'adinai ta barauniyar hanya ba. Gwamnati ta yi anfani da dakarun soja tare da kona na’urorin hakar ma'adinai da dai sauransu, amma yunkurin har ila yau yaci tura.

Gwamnatin Ghana Ta Gurfanar Da Wasu ‘Yan China Akan Laifukan Hakar Ma’adanai
Gwamnatin Ghana Ta Gurfanar Da Wasu ‘Yan China Akan Laifukan Hakar Ma’adanai

Masu ruwa da tsaki dai a kasar na ganin wannan matakin gurfanar da ‘yan kasar ta China da ake ganin sune ummul-haba’isin hakar ma'adinai ta barauniyar hanya zai taimaka sosai.

Mallam Baba Muhammad mai tattaro masu hakar ma'adinai a kananan filaye a kasar ya ce muddin gwamnati ta dau wannan matakin da muhimmanci, to shakka babu za a samu saukin wannan matsala.

Ya ce an kama wasu ‘yan Ghana masu hakar ma'adinai kuma suna sarka amma a duk lokacin da aka kama wani ‘dan China sai a sake ba da wani jinkiri ba, inji shi.

Shi kuwa babban jami'i a cibiyar horar da ilimin samar da zaman lafiyar kasa da kasa ta Kofi Annan International Peace Keeping Centre, Farfesa Kwasi Anning ya yi korafin cewa kasar China na da wata manufa ta gurbata ruwan kasar da sinadirai domin cocoa na kasar ya lalace.

Gwamnatin Ghana Ta Gurfanar Da Wasu ‘Yan China Akan Laifukan Hakar Ma’adanai
Gwamnatin Ghana Ta Gurfanar Da Wasu ‘Yan China Akan Laifukan Hakar Ma’adanai

Abinda ya kafa hujja da matakinda Japan ta dauka akan Ghana na rage yawan cocoa da take saya a kasar ta Ghana saboda gano wani bakon sinadari ciki. Ya jaddada bukatar gwamnati ta dau wannan mataki akan ‘yan China da muhimmanci domin kada suyi ma Ghana illa.

Aika-aikar wasu al’ummomin China na janyo ma kasar Ghana asarar kaddarori masu yawan gaske, ciki har da dazukan kasar dama asarar rayukan al’umma, yadda a baya bayan nan mahakar ma'adinai da wasu ‘yan China suka daina aiki akai ya rufta kan wasu mutanen Ghana su biyar, inda ya yi sanadin mutuwarsu.

Ghana dai ta tsinci kanta cikin jerin kasashen da ke fama da matsalar gurbataccen muhalli ta hanyar hakar ma'adanai, abin da ke lalata cocoa na kasar tare da ruwan sha da ma wasu kayan abinci.

Tuni tarayyar Turai ta yi barazanar haramta ma Ghana shigar da cocoa din ta a kasuwar nahiyar, muddan ba ta dauki mataki ba.

Saurari rahoton Hamza Adam:

Gwamnatin Ghana Ta Gurfanar Da Wasu ‘Yan China Akan Laifukan Hakar Ma’adanai.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

XS
SM
MD
LG