Kasuwannin hannayen jari na Amurka sun cira sama a lokacin da aka fara hada-hada yau alhamis, suka farfado daga subuta kasar da suka yi jiya, a bayan da wasu sabbin alkaluma na tattalin arziki a yau alhamis suka nuna cewa yawan ma’aikatan da kamfanonin Amurka ke sallama daga aiki yana raguwa.
Gwamnatin Amurka ta ce yawan mutanen da suka nemi tallafi a karon farko bayan da aka sallame su daga aiki a makon jiya, ya fadi kasa fiye da kowane lokaci cikin watanni 4 da suka shige. Manyan alkaluman hannayen jari na Amurka duk sun tashi sama da kimanin kashi daya da wani abu cikin 100 bayan da aka bude kasuwannin.
Su ma kasuwannin hannayen jari na kasashen Turai sun cira sama, bayan da tun farko suka nausa kasa, musamman bayan da ‘yan kasuwa suka yi ta sayar da hannayen jarin bankuna saboda fargabar cewa zasu zamo takardun banza ganin cewa basussukan da suke bin gwamnatocin Turai zasu iya gagara karbowa. Gwamnan babban bankin faransa, Christian Noyer ya nemi tabbatarwa da ‘yan kasuwa masu zuba jari cewa bankunan kasar su na nan da kwarinsu, yana mai fadin cewa gwajin da aka yi kwanakin baya ya nuna cewa bankunan su na da harsasai na kudi masu karfi.
Tun kafin nan kuwa, kasuwannin kasashen Asiya sun tankado kasa.
An shirya shugaba Barack Obama na Amurka zai yi tattaki zuwa Jihar Michigan dake tsakiyar wannan kasa nan gaba a yau alhamis domin ziyarar wata masana’antar fasahar zamani inda zai yi jawabi game da karfafa guiwar kirkiro sabbin fasahohi da nufin samar da sabbin ayyukan yi a cikin gida. Jiya laraba, shugaba Obama ya gana da shugaban babban bankin Amurka, Ben Bernanke, da sakataren Baitulmali Tim Geithner, domin tattauna yadda za a iya rage wagegen gibin kasafin kudin Amurka da kuma takalar matsalar mummunan bashin da ya taru a kan wasu kasashe masu amfani da takardar kudin Euro.