An tabbatar da ‘yan jarida da ma’aikatan yada labarai 88 suka mutu a kan aikinsu, saboda ana aunasu a kan rahotanni da suka bayar ko kuma suna aiki a wurare masu hatsari.
‘Yan jarida mata kuma na husakntar irin wannan hadari da takwarorin maza ke huskanta yayin da suke gudanar da ayyukansu, sai dai matan suna huskantar wata barazana da bai shafi mazan ba.
A wani taron kasa da kasa a kan walwalar ‘yan jarida da aka gudanar a London, mahalarta sun tattauna batutuwan barazana da kuma hanyar shawo kan lamarin.
Nadine Hoffman karamar darektan kungiyar kasa da kasa ta ‘yan jarida mata, ta fada cewa a wani bincike da aka gudanar a bara, yace ‘yan jarida mata dari shida suka ce sun huskanci barazana ta yanar gizo. Tace yawanci barzana ce a kan lalata da matan da kuma cin zarafi ga ‘ya’ya mata.