Kokarin da Rasha ke yi na bijirewa takunkumin da Amurka ta kakabawa Iran da alama bai yi nasara ba, a yayinda da kwararru a fannin makamashi ke cewa Rasha bata siya mai daga Iran ba kwanan nan, a zaman wani bangaren yarjejeniyar da aka cimma da Tehran a shekarar 2014.
Kafofin yada labaran Rasha sun ce a karkashen yarjejeniyar da aka cimma a watan Agustan shekarar 2014, wadda ba a wallafa dukan ta ba, Rasha ta amince ta sayi mai daga Iran, don ta iya kaiwa masu bukata daga wasu kasashen.
A yayinda ita kuma Iran zata yi amfani da kudaden da ta samu daga Rasha ta sayi kayayyakin Rashar. Kafafen yada labaran Iran sun ce rabin kudaden da aka samu daga Rasha kawai za yi amfani da su wajen sayen kayayyakin Rashar.
Bangarorin biyu sun cinma yarjejeniyar da suka kira “sayen mai don kaya” a wani lokaci da aka sanyawa Iran takunkumi, akan man ta da take fitarwa waje. Rasha ta ce an yi yarjejeniyar ne da zummar bunkasa dangantakar kasuwanci da Iran, kasar da ta dade ta na sayen makaman Rasha.
Facebook Forum