Hukumomi a birnin Kyoto na kasar Japan yanzu sun ce akalla mutane 23 ko dai sun mutu, ko kuma ba sa cikin hayyacin su, bayan tashin wata gobara da ake kyautata zaton hari ne akan wani gidan hada fina-finan wasan yara.
Ma’aikatan kwana-kwana sun ce an tabbatar da mutuwar mutane 13, bayan haka an kuma gano mutane 10 da basa cikin hayyacinsu, kuna ba sa nuna alamun suna da rai a saman benen ginin mai hawa uku, inda kamfanin Kyoto Animation Production ya ke, da kuma matakalar zuwa soron ginin.
Adadin mutanen da gobarar ta shafa ya hada da fiye da wasu su 30 da suka samu munanan raunuka, wasunsu su na cikin mawuyacin hali.
'Yan sanda sun ce gobarar ta fara ne a lokacin da wani mutum ya shiga cikin ginin, ya jika shi da wani abu mai saurin kama wuta, ya na ihu yana fadin “Ku Mutu” a yayin da ya tada wutar. Kusan mutane 70 ke cikin ginin a lokacin da gobarar ta tashi.
Wanda ake zargi da aikata laifin, wanda kafar yada labaran Kyoto ta bayyana a matsayin wani mutum dan shekaru 41 da haihuwa, shi ma ya sami rauni kuma an kai shi wani asibiti dake kusa da wurin don jinya.
Facebook Forum