Koriya ta Arewa ta caccaki shirin da Amurka ke yi na gudanar da wani atisayen soji, na hadin gwiwa da Koriya ta Kudu a cikin wata mai zuwa, ta na ganin wannan atisayen na iya kawo cikas ga shirin ganawa game da batun makaman nukiliya da koriya ta arewa ke shirin yi da Amurka.
A wata sanarwa daga kamfanin dillancin labaran Korean Central News Agency, ma’aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa, ta fada a yau Talata cewa yin wannan atisayen zai saba yarjejeniyar da aka cinma a bara tsakanin Donald Trump da Kim Jong Un a birnin Singapore.
“Za mu duba makomar matakan Amurka, kuma zamu yanke shawara game da tattaunawar da ake shirin yi tsakanin Koriya ta Arewa da Amurka” a cewar sanarwar da wani mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar da ba a bayyan sunan sa ba.
Amurka da Koriya ta Arewa sun amince su tattauna, biyo bayan wata ganawa da aka shirya a gurguje a watan jiya tsakanin Trump da Kim a yankin da ba ayyukan soja wanda ya raba koriya ta Arewa da koriya ta kudu.
Facebook Forum