An kama wani malamin addinin Islama wanda ake zargi da kafa wata kungiyar ‘yan ta’adda wacce aka dora mata laifin harin Mumbai da aka kai a shekarar 2008.
Hukumomin Pakistan sun ce an kama Hafiz Saeed a yau Laraba a mahaifarsa da ke Lardin Punjab a kusa da wani gari da ake kira Gujranwala.
Ana zargin kungiyar Saeed mai suna Lashkar-e-Talib da kai hare-hare a cibiyar kasuwancin kasar ta India, wadanda suka hallaka sama da mutum dari 170 suka kuma jikkata sama da mutum 300 cikin kwanaki hudu.
Amurka ta yi tayin ba da tukwicin dala miliyan goma ga duk wanda ya ba da bayanan da za su kai ga kama Saeed.
Wannan kamu da aka yi wa Saeed, na zuwa ne kwanaki kafin ziyarar da Firai minista Imran Khan, zai kawo nan Washington.
Facebook Forum