FIFA Ta Fitar Da Kasashen Da Za Su Karbi Bakuncin Gasar Cin Kofin Duniya Ta 2030

Wakilan kasashen Uruguay, Argentina da Paraguay, wadanda za su karbi bakuncin gasar 2030

Wani muhimmin abin burgewa na hadin nahiyoyi uku da ba a taba ganin irinsa ba shi ne, yadda za a bude wasan a Uruguay, kasar da ta fara karbar bakuncin gasar a duniya.

Za a buga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2030 a Turai da Afirka a cewar hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA.

Wani abin mamaki shi ne an yi karin Kudancin Amurka a yarjejeniyar ba da damar daukan gasar kwallon kafa ta maza da a fara yin bikin cika shekaru 100 a Uruguay.

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta cimma yarjejeniya a ranar Laraba tsakanin shugabannin kungiyoyin kwallon kafar don karbar dan takara daya kacal domin karbar bakuncin gasar ta 2030 a kasashe shida, in ji hukumar wasannin.

Tayin Sifaniya da Portugal na daukar nauyin gasar ya karu da karin Morocco a wannan shekara kuma yanzu haka ya hada da kishiyoyinsu Argentina da Paraguay da Uruguay da suka dade suna neman tikitin.

FIFA ta ce dukkan kungiyoyin kasashe shida za su samu shiga gasar da za ta kunshi kungiyoyi 48.

Wani muhimmin abin burgewa na hadin nahiyoyi uku da ba a taba ganin irinsa ba shi ne, budewar gasar a babban birnin kasar Uruguay na Montevideo, inda filin wasan Centenario ya karbi bakuncin wasan karshe na gasar cin kofin duniya na farko da aka yi a shekarar 1930.

-AP