Kasashe takwas na neman kujerar Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya

Ban Ki-moon babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya da zai kare wa'adinsa karshen wannan shekarar

Yanzu hankalin kasashen duniya ya koma kan zaben babban sakataren Majalisar Dikin Duniya da za'a yi kwanan nan yayinda wa'adin Ban Ki-moon ke cika

Kawo yanzu kasashe takwas ne suka gabatar da sunayen wadanda suke son a zaba ya maye gurbin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon wanda wa'adinsa zai cika kwanan nan..

A karon farko sabanin abun da aka saba ganin za'a zabi babban sakataren a bainar jama'a. Da can a cikin sirri ake yin zaben kana a sanar da duniya.

Daga yau Talata za'a dinga ba kowane dan takara minti goma na yin jawabi akan cancantar zama sakataren na Majalisar Dinkin Duniya da yanzu take da shekaru 72.

Duk wanda aka zaba sai watan Janairun shekarar 2017 zai dare kujerar