. Wanda yace wannan abu ne muhimmi ga mutanen kasar da kuma ita kanta kotun duniya mai hukunta laifufukan kasa da kasa.
Mista Ban yace, wannan hukunci ya nuna karara duk wanda ya aikata laifi bas hi da maboyar da zai tserewa hukuncin da al’ummar duniya suka nemi a yanke masa bayan kama shi da laifi, don fuskantar sheri’ar da ta dace da shi.
Kotun da a baya aka kafata don sauraron kararrakin tsohuwar kasar Yogoslavia da ta rikide zuwa kotun duniya, ta yankewa Karadzic hukuncin shekaru 40 a gidan yari sakamakon samunsa da laifin aikata kisan kare dangi da wasu laifuffuka guda 9.
A yanzu dai shekarun mai laifin 70 ne da haihhuwa, wanda in za a iya tunawa shine ya jagoranci kisan kiyashin da aka yiwa Musulman Bosnia maza da kanann yara a shekarar 1992 zuwa 1995 a yakin da ya hallaka sama da mutane dubu 100.