Libya Ta Koro 'Yan Najeriya, Mali 463 Zuwa Nijar

Kasar Libya Ta Mayar Da 'Yan Cirani Daga Najeriya Da Mali Zuwa Jamhuriyar Nijar

Kafin isar 'yan ci-ranin a arewacin Nijar sun tagayyara a kasar Libya ciki har da mata da ƙananan yara sama da 100, inda kungiyoyin ayyukan jin kai suka nuna damuwa game da 'yan Najeriya tare da yin kira ga hukumonin Nijar da su gaggauta daukar matakan daukar nauyin wadannan mutane.

Kasar Nijar a duk rana ta na fama da kwararar bakin haure daga arewacin kasar musanman wadanda ake korowa daga Aljeriya.

An dai ce jami’ai sun balle kofar wani gidan da wasu mutanen suke zaune tare da tafiya da su bayan kuwa kowannen su suna cikin gida sun shafe shekaru a kasar ta Libiya.

Kasar Libya Ta Mayar Da 'Yan Cirani Daga Najeriya Da Mali Zuwa Jamhuriyar Nijar

Suka ce jami’an sun kwace duk wasu shaidu dake tabbatar da zaman su a kasar sannan kuma suka tsare su tare da mata kafin daga bisani suka jefa su cikin mutanen da aka tilasta musu fita kasar.

kungiyoyin kare hakkin bil’adama na ganin akwai bukatar gwamnatocin kasashen yankin Afirka ta Yamma da su tura wata tawaga ta jami’ai domin tattauna yadda za’a bullo ma lamarin musamman tunda akwai dangantaka mai kyau tsakanin kasar Libiya da wasu kasashen na Afirka irin su Najeriya da Nijar.

To saidai wadanda aka koro na fatan samun ayyukan yi a kasashen su domin acewar su rashin aikin yi ne ke sanya su wadannan tafiye tafiyen zuwa wasu kasashen

Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud:

Your browser doesn’t support HTML5

Libya Ta Koro 'Yan Najeriya, Mali 463 Zuwa Nijar