Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cafke Wani Kasurgumin Mai Safarar Bakin Haure Zuwa Turai Dan Kasar Libiya


Safarar bakin haure
Safarar bakin haure

Jami'an 'yan sanda sun cafke wani dan kasar Libiya mai shekaru 29  mai jagorantar safarar bakin haure da ke bi ta Nijar zuwa Turai.

An kama mutumin ne bayan wani bincike na hadin gwiwa tsakanin 'yan sandan Nijar da Faransa da Spain kamar yadda wata majiyar 'yan sandan Faransa ta bayyana cewar wanda aka kaman yana aika ‘yan ci-rani sittin a kowane mako har tsawon shekaru bakwai.

Galibin su daga kasashen yankunan yammaci da tsakiyar Afirka. To sai dai kungiyar tsofaffin da suka yi safarar bakin haure sun bayyana cewa rashin cika alkawarin da kungiyar Tarayyar Turai da gwamnatin Nijar suka yi na daga cikin dalillan da yassa matasan har yanzu ke safarar bakin haure ta arewacin Nijar.

Safarar bakin haure
Safarar bakin haure

An kama matashin ne da ya shahara wajen aika bakin haure daga Nijar zuwa Libiya da Algeria a Agadas dake arewacin Nijar, wanda aka kaman ya shafe tsawon shekaru yana aika bakin haure zuwa kasashe dake makwabtaka da Nijar. Galibin bakin haure da ke sha'awar tafiya turai na fitowa ne daga yammaci da tsakiyar Africa.

A baya ana daukar bakin hauren ne a cikin motocin dakon kaya a kaisu Nijar tare da kaucewa manyan birane, daga nan sai a wuce da su Libiya da Algeria. Malan Mohamed Adamu wani matashi ne da har yanzu bai daina safarar bakin haure ba duk da irin matakkan da mahukunta ke dauka.

Amadu Umaru wanda shine shugaban mutanen da suka yi watsi da sana’ar safarar bakin haure ya bayyana cewa idan ana son a kawo karshen wanna abu, wajibi ne Tarayyar Turai da hukumomi a Nijar su aiwatar alkaura da suka dauka domin an sha daukar alkawari ba tare da an cikawa ba da kuma kafa kamfanonin da za’a dauki matasan aiki. Da haka ne kawai zasu daina wannan aikin kuma shine mafita.

Arewacin hamadar Nijar ya yi kaurin suna wajen safarar bakin haure da muggan kwayoyi da makamai kuma yana tattare da kungiyoyi masu ikirarin jihadi.

Saurari rahoton Hamid Mahmud :

RAHOTON SAFARA.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG