Kasar Angola Ta Yi Horon karshe Don Karawa Da Kasar Ghana

Black stars

Palacas Negras da ke shirya kece reni da ‘yan wasan Black Stars na Ghana a wassanin neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika, ta yi horon ne da karfe bakwai na dare.

Kasar Angola ta sauka birnin kumasi daga Algeria, inda ‘yan wasanta suka yada zango don shirin wasanni guda biyu da zata yi.

Pedro Goncalves ya samu duk ‘yan wasan da ya gayyata don fuskantar Black Stars, bayan maye gurbin Nurio Nelson Da Luz da wasu ‘yan wasa da suka hada da Augusto Carneiro, da Loida Augusto, da kuma Geraldo Cost Bartolomeu.

Goncalves dai ya amince cewa wasa da Ghana zai yi wuya, a saboda haka akwai bukatar ‘yan wasansa su yi kamar suna yi don samun shiga gasar cin kofin Afrika.

"Muna sane da irin wahalar da zamu fuskanta, amma a shirye muke don wasa a Kumasi," abinda Goncalves ya fada wa ‘yan jarida kenan.