A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na twitter, hukumar kwallon kafar Najeriya ta NFF, ta tabbatar da isowar zaratan ‘yan wasan na ta a sansanin atisaye da ke Abuja ya zuwa ranar Litinin, ciki har da Alex Iwobi, Wilfred Ndidi, Ademola Lookman da Kelechi Iheanacho.
Haka kuma ana dakon isowar sauran ‘yan wasan kasar kamar kaftin Ahmed Musa, Moses Simon, Keneth Omerou da Paul Onuachu.
‘Yan Najeriyar da dama ne dai yanzu haka suke dokin ganin zuwan matashin dan wasan kasar Victor Osimhen, da ke taka leda a kungiyar Napoli ta kasar Italiya, wanda shi ma ake sa ran zuwansa domin wasannin.
Najeriyar wadda ta taba lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka sau uku a tarihi, ita ce za ta karbi bakuncin kasar Guinea Bissau a wasan farko da za’a buga a filin wasa na Moshood Abiola a ranar 24 ga wannan wata na Maris, kafin su tashi zuwa Guinea Bissau din domin buga wasa ta biyu.
A kasar Ingila kuma zaratan ‘yan wasa uku ne suka janye daga tawagar ‘yan wasan kasar da za su buga wasannin neman gurbin gasar cin kofin nahiyar turai ta shjekara ta 2024.
Marcus Rashford na Manchester United, da Mason Mount na Chelsea da kuma Nick Pope na kungiyar Newcastle, duk suna fama ne da raunuka iri daban-daban, wanda ya sa tilas aka fitar da sunayensu daga jerin ‘yan wasan da za su buga wasannin.
Rashford ya sammi rauni ne a wasan kusa da na karshe na gasar FA da kungiyarsa ta United ta yi nasarar doke Fulham a ranar Lahadi, yayin da shi kuma Mount, a yanzu yake farfadowa daga raunin da ya dan jima yana fama da shi. Da farko ma an saka da sunansa a cikin ‘yan wasan, to amma kuma kungiyarsa ta Chelsea ta nuna rashin amincewa da haka, kasancewar dan wasan bai ida murmurewa ba.
Kungiyar kwallon kafar Tottenham ta Ingila ta ce ba zata iya sayar da shahararren dan wasanta Harry Kane ba, muddin ba za’a iya biyan zunzurutun kudi har fam miliyan 100 ba a wannan bazarar.
Kane mai shekaru 29 zai shiga shekara ta karshe ta kwantaraginsa a karshen wannan kakar wasannin, kuma ana hasashen cewa Tottenham ta tsala wannan kudin ne don hanawa wasu kungiyoyi sayen dan wasan.
Kungiyoyi da dama ne suk nuna sha’awar samun Kane, ciki har da Manchester United da yanzu haka take kan gaba, to amma wasu rahotanni na bayyana cewa Tottenham ba ta bukatar sayar da dan wasan a kungiyoyi abokan hamayyarsu.