Kungiyar ta yanke wasu shawarwari ne akan juye-juyen mulki a Afirka ta Yamma da matsalolin tsaron da ya mamaye kasashe da dama.
Malam Garba Shehu kakaki a fadar gwamnatin Najeriya ya yi mana karin bayani bayan da shugaban kasar Buhari ya sauka a birnin tarayya Abuja.
Garba Shehu ya fara da cewa wannan karon, shugabannin sun hadu da juna ba kamar yadda da suka yi ba ta yanar gizo saboda yaduwar annobar coronavirus.
Ya ce sun tattauna akan batutuwa da dama musamman akan batun juye-juyen mulki da ke yawan fa faruwa yanzu a Afirka ta Yamma da kuma sha’anin rashin tsaro sakamakon hare-hauren ‘yan bindiga.
Ya kara da cewa shugaba Buhari ya yi magana akan tsaro da yadda ake kashe makudan kudi don yaki da rashin tsaro amma har yanzu da saura, kuma yayi magana akan taimakawa a wurare dabam-dabam a kara hadin kai da sauran kasashen.
Saurari rahoto cikin sauti daga Umar Farouk Musa daga Abuja:
Your browser doesn’t support HTML5