Farfesa Shehu ya bayyana haka ne a hirar shi da Muryar Amurka biyo bayan girke dakaru da shirin ko ta kwana da kasashen su ke yi a kan iyakar Rasha da Ukrain, lamarin da ya dauki hankalin kasashen duniya.
Bisa ga cewarshi, jama’a suna ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum da suka saba kuma ofishin jakadancin Najeriya na ci gaba da gudanar da ayyuka akasin rahotannin da ake yayatawa.
Jakadan Najeriya a Rasha ya bayyana cewa, jama’a suna zaune hankali kwance a halin yanzu sabili da dalilai biyu. Na farko, makon da ya gabata, Ministan harkokin kasashen ketare na kasar Rasha, Sergey Viktorovich Lavrov ya sanar da cewa, Rasha bata da shirin kai hari ko kuma mamaye Ukrain, sai dai Ministan harkokin kasashen wajen ya bayyana cewa, Rasha tana da hurumi da ‘yancin kare kanta idan aka taba ta. Bisa la’akari da abinda ke faruwa a kan iyaka da Ukrain, dalili ke nan da ya sa ta yi damara tana zaune da shiri.
Dalili na biyu da ‘yan Najeriya su ke zaune hankali kwance a Rasha a cikin wannan yanayin bisa ga cewar Farfesa Shehu shine, shugaban kasar Ukrain Volodymyr Oleksandrovych Zelenskyy da kansa ya bada sanarwar cewa, irin fargaban abinda mutane suke ji ko kuma fada a kafofin sadarwa ba haka ba ne, domin su basu fuskanci barazana da fargaba a cikin kasar Ukrain kamar yadda ake yayatawa ba. Bisa ga cewar shugaban kasar Ukrain sun yi ammana cewa, za a sami saukin halin da ake ciki.
Farfesa Shehu ya ce wadannan bayanan biyu da aka yi su ka sa, jama’a ke kyautata zaton cewa, abinda ke tafe tsakanin Rasha da Ukrain da Amerika da sauran kasashe, abu ne da ba zai zama da razanarwa ba.
Dangane da yadda lamarin zai iya shafar harkokin diplomasiyan kasashen duniya, Farfesa Shehu ya ce babu shakka akwai bukatar karatun ta natsu domin matakin da za a dauka zai iya shafar dangantaka, da kuma yanayin da ake ciki, ko kuma kalubalai da ake fuskanta a wadansu kasashen duniya.
Saurari cikakkiyar hirar cikin sauti: