Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC Ta Kafa Kwamitin Sasanta Rikicin Kano Karkashin Jagorancin Ganduje


Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje (Facebook/Gwamnatin Kano)
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje (Facebook/Gwamnatin Kano)

Tsohon gwamnan jihar ta Kano Sanata Ibrahim Shekarau ne mataimakin gwamna Ganduje a kwamitin.

Hedkwatar jam’iyyar APC a Najeriya ta kafa wani kwamiti da zai aiwatar da jadawalin da aka tsara don warware rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar a jihar Kano.

Kwamitin rikon kwaryar jam’iyyar ta APC na kasa karkashin gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ne ya kafa kwamitin mai mutum biyar daga matakin kasa da jihar, karkashin jagorancin Gwamna Umar Abdullahi Ganduje.

Tsohon gwamnan jihar ta Kano Malam Ibrahim Shekarau ne mataimakinsa.

Kwamishinan yada labaran jihar Kano Comrade Muhammed Garba ne ya wallafa kwafin wasikar da hedkwatar jam’iyyar ta aikawa Ganduje a ranar Litinin dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan kwamitin rikon kwaryar jam’iyyar ta APC Abdullahi Gashua.

Sanarwar ta ce matsayar da aka cimma a zaman sulhun da aka yi da dukkan bangarorin biyu a daren ranar Litinin, ta yi nuni da cewa Ganduje ne jagoran jam’iyyar ta APC a Kano, inda aka yi kira a gare shi da cewa, a matsayinsa na shugaba, ya yi tafiya da duk masu ruwa da tsaki a jam’iyyar.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle da tsohon kakakin majalisar wakilan Najeriya Yakubu Dogara sai Senator Abba Ali. Baya ga haka sakatariyar jam’iyyar za ta turo wakili na cikon biyar.

Kwamitin zai fara zama a jihar ta Kano, inda ake sa ran zai mika rahoto cikin kwana bakwai.

Jam’iyyar APC a jihar ta Kano ta tsunduma cikin rikicin cikin gida inda aka samu bangaren Ganduje da na Shekarau da kowannen su yake ikirarin shi ne jagora.

XS
SM
MD
LG