SOKOTO, NIGERIA - A halin yanzu dai ‘yan Najeriya sun tsinci kansu cikin mawuyacin hali na karancin kudade da za su yi lalurar yau da kullum saboda sabon tsarin da babban bankin kasar ya soma amfani da shi.
To amma ‘yan magana na cewa dole uwar na ki, kuma rashin uwa kan sa a nemi uwar daki, yanzu haka wasu ‘yan kasar yanayin ya tilasta su soma amfani da tsarin musayar kaya domin karbar wasu kaya da suke bukata.
Wasu jama'a kuma musamman mazauna garuruwan da ke da iyakoki da Jamhuriyar Nijar suna amfani da kudin saifa na Nijar wajen cinikayyar su, kamar yadda wani mutum Muhammad Aliyu Illela ya sheda mana.
Haka kuma shi ma wani mutumin Kamba ta Jihar Kebbi ya tabbatar mana da cewa dole ce ke sa su amfani da kudin na Nijar.
To sai dai masana tattalin arziki na cewa ci gaba da irin wannan tsari na da hadari ga tattalin arzikin Najeriya.
Bashir Muhammad Achida na jami'ar Usmanu Danfodiyo na ganin cewa wannan tsarin da babban bankin Najeriya ya soma aiki da shi tsari ne mai kyau.
Da yake gwamnatin Najeriya ta kalubalanci hukuncin da kotun koli ta yi na dakatar da amfani da wa'adin goma ga Fabrairu a zaman lokacin da za a daina karbar tsofaffin kudi, da yawa ‘yan kasa sun zura ido don ganin yadda lamarin zai kasance da yake wa'adin goma ga watan ya cika.
Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5