Ranar Litinin ne hukumar kwallon kafar Najeriya NFF tayi kira ga ‘yan Najeriya da su yi hakuri da babban kochin kungiyar Super Eagles Sunday Oliseh, alokacin da yake kokarin gina tawagarsa.
Da yake magana da kamfanin dillancin labaran Najeriya, sakataren hukumar NFF, Mohammed Sanusi yace wasannin da kungiyar tayi bai kai yawan da za’a iya yanke hukunci kan ko Oliseh zai iya shugabantar kungiyar ba.
Ya ci gaba da cewa nasarar da Super Eagles suka samu kan kasar Kamaru a wasansu da aka tashi uku da nema a wasan kawance na ranar Lahadi, na nunin yadda kungiyar ta ‘dauki darasi a wasansu na baya inda suka sha kashi a hannun kasar Congo.
Duk yake dai wasanni biyu kacal suka buga kuma baikamata ba a fara yanke hukunci kan Sunday Oliseh ba tukunna, dole ne mutane su bashi dama su kuma kara yin hakuri, domin ci gaban da aka samu a wasa na biyu da Kamaru na nunin cewa komai zai yi kyau nan gaba.
Hukumar kwallon Najeriya NFF bata sauri wajen ganin sakamako cikin gaggawa daga Sunday Oliseh, tunda ‘yan wasan suna kara kwarewa.