Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Super Eagles Sun Huce Haushi Kan Kamaru


Magoya bayan Super Eagles na Najeriya
Magoya bayan Super Eagles na Najeriya

Najeriya ta lallasa Kamaru da ci 3-0 a wasan sada zmunic da aka yi a filin wasa na Machtens-Stadion da ke Belgium a jiya Lahadi.

Efe Ambrsoe da Moses Simon da kuma Odion Ighalo ne suka zirawa Super Eagles kwallayenta.

Wannan nasara na zuwa ne bayan da Najeriya itama ta sha kashi a hanun Jamhuriyar Dimokradiyar Congo da ci 2-0 a ranar Larabar da ta gabata.

Kamarun dai ta je wasan da ne da ‘yan wasa irinsu Stephane Mbia da Benjamin Moukandjo da Sebastine Bassong da kuma Vincent Aboubacar, wadanda suka yi ta fama da takwarorinsu ‘yan Najeriya ba tare da sun kai ga gaci ba.

Shi dai Ambrose ya yi amfani da kansa ne wajen zira kwallo a minti na 39 bayan da Mikel Obi ya doko kwallon, wadda ta baiwa Najeriya damar zira kwallon farko kafin a je hutun rabin lokaci.

Yunkurin rama kwallon ya dishe ga kamaru bayan da aka baiwa dan wasanta Mbia katin sallama a minti na 47.

Hakan kuma ya zama wata dama ce ga ‘yan wasan Super Eagles, wadanda suka kara wasu kwallaye biyu.

Yanzu haka, mai horar da ‘yan wasan Najeriya, Sunday Oliseh zai fara shirye shiryen wasannin fidda gwanayen da za su halarci gasar cin kofin duniya da za a yi a shekarar 2018, inda za su kara da Djbouti ko kuma Swaziland.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG