Babban Kocin kungiyar Enyimba, Kadiri Ikhana, har yanzu na da kwarin gwiwa kan cewa tawagarsa ce za ta zama zakaran wasannin Firimiya Lig da ake na manyan kungiyoyin Najeriya.
Kungiyar Heartlance ta sami nasara da ci 2-1 kan Enyimba a wasan da suka yi ranar Lahadi a Owerri. Ikhana dai ya bayyana cewa rashin sa’ar wasan da aka yi na Lahadin ya kara sa musu matsin lamba a sansanin su, amma ya nace kan cewa zasu juya akalar hakan kuma su sami zama zakaran gasar a karo na bakwai.
Ikhana yace, “zan fadi haka ne da kwarin gwiwa cewa kofin wannan gasar na kungiyar Enyimbane, duk kuwa da cewa bamu samu nasara ba a wasanmu na baya.” Ya kuma ci gaba da cewa muna bukatar samun nasara ko da sau dayane domin mu samu mu lashe sauran wasannin da muke da su a gida, sannan mu je waje mu samu lashe wasa daya ko biyu.
Har yanzu dai kungiyar Enyimba ce kan gaba akan teburin gasar, ta na da maki uku gaban kungiyar da ta ke bayanta, wato Warri Wolves.