Hukumar kwallon kafar nahiyar Afrika, CAF, ta fitar da dogon jerin sunayen ‘yan wasan kwallon kafa 37 da aka ware domin a tantance wadanda zai lashe kyautar wanda ya fi iya taka kwallo a nahiyar na bana.
Daga cikin wadannan ‘yan wasa akwai mai tsaron ragar Najeriya Vincent Enyeama da Kyaftin Ahmed Musa da Yaya Toure na Ivory Coast da ke rike da kambun wannan gasa da kuma Andrew Ayew na kasar Ghana.
Enyeama, wanda ya bayyana ritayarsa a fagen wasa na kasa da kasa, ya kasance daya daga cikin fitattun masu tsaron raga a nahiyar ta Afrika da kuma turai, inda ya ke taka leda a gasar Ligue 1 a kungiyar Lille da ke Faransa.
Shi kuwa Musa ya kasance zakara ne a CSKA Moscow yayin da Toure ya taba lashe wannan gasa sau hudu ciki har da shekaru uku na baya da su ka gabata a jere.
Ga cikakken sunayanen ‘yan wasan da hukumar ta CAF ta fitar:
1. Ahmed Musa CSKA Moscow, Russia Nigeria
2. Andre Ayew Swansea City, England Ghana
3. Aymen ABDENNOUR FC Valence, Spain Tunisia
4. Baghdad Bonjah Étoile du Sahel, Tunisia Algeria
5. Bassem Morsi Zamalek, Egypt Egypt
6. Chrisitian Atsu Bournemouth, England Ghana
7. Dieu Merci Mbokani Norwich, England D.R Congo
8. El Arbi Hillel Soudani Dynamo Zagreb, Croatia Algeria
9. Faouzi Ghoulam Napoli, Italy Algeria
10. Férébory Doré Angers, France Congo
11. Gervais Yao Kouassi Rome, Italy Cote d’Ivoire
12. Ibrahima Traoré Borussia Mönchengladbach, Germany Guinea
13. Javier Balboa Al-Faisaly, Saudi Arabia Equatorial Guinea
14. Héldon Ramos Rio Ave, Portugal Cape Verde
15. Mame Diouf Stoke City, England Senegal
16. Max Alain Gradel Bournemouth, England Cote d’Ivoire
17. Mehdi Benatia Bayern Munich, Germany Morocco
18. Modather Al Tayeb “Karika” Al Hilal, Sudan Sudan
19. Mohamed Salah As Roma, Italy Egypt
20. Nicolas Nkoulou Marseille, France Cameroon
21. Pierre-Emerick Aubameyang Borussia Dortmund, Germany Gabon
22. Robert Kidiaba T.P Mazembe, D.R Congo D.R Congo
23. Rudy Gestede Aston Villa, England Benin
24. Riyad Mahrez Leicester City, England Algeria
25. Sadio Mané Southampton, England Senegal
26. Serge AURIER Paris Saint Germain, France Côte d’Ivoire
27. Seydou keita Rome, Italy Mali
28. Sofiane FEGHOULI Valence, Spain Algeria
29. Stéphane Mbia Trabzonspor, Turkey Cameroon
30. Thievy Bifouma Granada, Spain Congo
31. Victor Wanyama Southampton, England Kenya
32. Vincent Aboubakar Porto, Portugal Cameroon
33. Vincent Enyeama Lille, France Nigeria
34. Yacine Brahimi Porto, Portugal Algeria
35. Yannick Bolasie Crystal Palace, England RD Congo
36. Yasine Chikhaoui Al-Gharafa, Qatar Tunisia
37. Yaya Toure Man City, England Cot d’Ivoire.