ABUJA, NIGERIA - A ranar Alhamis ne babbar kotun a birnin tarayya Abuja ta ba da belin tsohon ministan sufurin jiragen saman Najeriya, Hadi Sirika tare da ‘ya da surukinsa biyo bayan kin amincewa da aikata laifin da gwamnatin Najeriya ke mu su na karkatar da kudadden da suka kai Naira biliyan 2.7 bisa sharuddan kudin belin naira miliyan 100 kowannensu tare da masu tsaya musu su biyu.
Ana zargin tsohon ministan da yin amfani da ofishinsa wajen ba da kwangilar naira biliyan biyu da miliyan 700 ba bisa ka’ida ba ga ‘yarsa, wato surukinsa karkashin kamfanin Al-Duraq lamarin da tuni ‘yan Najeriya ke ta yin kiraye-kirayen a tabbatar da an yi adalci wajen yin shari’ar.
A cewar mai sharhi a kan al’amurran siyasa, Abubakar Muhammad wanda aka fi sani da Abujega ba da belin Sirika, diya da surukinsa bai zo da mamaki ba ganin rashin karfin dokar kasar.
Shugaban kungiyar tabbatar da kare hakkin bil’adama yaki da rashawa, neman gaskiya da adalci a Najeriya, Auwal Musa Rafsanjani ya ce dole ne a yi ba-sani-ba-sabo a shari’ar Hadi Sirika kuma za su ci gaba da marawa hukumomin gwamnati da ke yaki da cin hanci da rashawa baya kuma ba za’a lamunce batun kawo tsarin "Plea Bargain" a shari’ar tsohon ministan sufurin jiragen saman Najeriyar ba.
A fuskar doka kuwa, fitaccen masanin kundin tsarin mulki a Najeriya, Barr. Mainasara Kogo ya bayyana cewa sashe na 15 sakin sashe na 5 na tsarin mulkin Najeriya ya dora wajibci a kan kowanne jami’in gwamnati ya yaki cin hanci da rashawa kuma ganin yadda mutane ke fargabar za’a koma gidan jiya na yin amfani da tsarin plea bargain, abu ne da ya sabawa doka saboda haka a gaggautan yin shari’ar ta fuskar adalci.
Ko a watan Febrairun EFCC ta kama ‘dan uwan Sirika Abubakar Sirika bisa zargin badakalar kwangila a ma’aikatar sufurin jiragen sama wanda tsohon ministan ya bai wa wani kamfani mai suna Engirios Nigeria Limited mallakin kaninsa, kafin wannan shari’ar da ya kai ga ba da belinsa.
Kazalika a lokacin da ya ke rike da mukamin minista, Sirika ya fuskanci zarge-zarge masu alaka da hada baki, yin amfani da alfarmar kujerarsa wajen aikata ba daidai ba, karkatar da kudaden jama’a da suka kai Naira biliyan 8 da doriya da dai sauransu. Sirika ya musanta zarge-zargen.
Saurari cikakken rahoto daga Halima Abdulrauf:
Your browser doesn’t support HTML5