ABUJA, NIGERIA - Hadi Sirika ya ce gaskiyar magana salon talla ne daga masu hannun jarin kamfanin ya sa a ka kawo jirgin guda daya ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe a Abuja kuma hakan ba sabon abu ba ne.
Tsohon ministan wanda ya ce gwamnatin Najeriya na da hannun jarin kashi 5% kacal a kamfanin sauran 95% na ‘yan kasuwa ne da mafi tsoka na Ethiopia ne.
A zaman karshe da kwamitin jiragen sama na majalisar dattawa ta 9 da ta kare mulki ta yi kan kamfanin jirgin na Najeriya Air, ya nuna cewa ba a gayyace su kaddamarwar ba ko ba a saka su a tsarin ba gaba daya.
Shugabar kwamitin ce Biodum Olujimi ke cewa gaba daya an gudanar da tsarin Najeriya a boye inda aka gabatar da shi cikin kumbiya-kumbiya a matsayin jirgin sama na kasa da hakan ya yi hannun riga da ka’idojin aikin jirgi da dokokin kasa da kasa da ke jagorantar harkar jiragen sama.
Hakika wannan a wajen kwamitin zubar da mutunci ne.
An tambayi Hadi Sirika shin mene ne na gaggawa da sai kusan jajiberin sauka daga mulki ya dage wajen kawo samfurin jirgin maimakon jiran sabuwar gwamnati?
Sirika ya ce ai har sa’ar karshe ta gwamnati za a iya yin aiki don haka ba zai yi wu a bar wani abu mai muhimmanci don lokaci ya kure ba.
Mukaddashin shugaban kamfanin Dapo Olumide ya ce ba kamar yadda 'yan kafafen labarun sada zumunta su ka yada ba cewa an kaddamar da jirgi mallakar kamfanin Najeriya Air; yadda lamarin ya ke an yi shatar jirgin ne don bukin nuna alamar sabon kamfanin.
Dapo Olumide ya ce har dai kamfanin zai samu rejista sai ya mallaki jirage uku kuma shi aikin da a ka saka shi shi ne samarwa kamfanin lasisin izinin tashiin jirgi.
Dapo ya ce ai tun 2018 hotuna da zane-zane kawai ake gani na Najeriya eya don haka kenan a ka zo da samfuri don a ga yanda jirgin zai kasance.
A tarihi dai Najeriya na da kamfanin ta na Nigeria Airways inda a ka fatar Najeriya Air zai maye gurbin sa, ashe ko an samu nasara gwamnati na da kashi 5% kacal na jarin sa.
Saurari cikakken rahoro daga Nasiru Adamu El-Hikaya: