Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Bada Belin Sirika Bayan Musanta Zargin Badakalar Biliyan 2.7


Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Saman Najeriya, Hadi Sirika
Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Saman Najeriya, Hadi Sirika

An gurfanar da Hadi Sirika ne a gaban Mai Shari’a Sylvanus Oriji na babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Abuja tare da diyarsa, Fatima, da surkinsa, Jalal Sule Hamma, da wani kamfani mai suna Al Buraq Global Investment Limited.

Kotu ta bada belin tsohon ministan Sufurin Jiragen Saman Najeriya, Hadi Sirika biyo bayan musanta zargin aikata laifin almundahana da ya shafi kusan Naira biliyan 2.7 da Gwamnatin tarayya ke masa.

An gurfanar da Hadi Sirika ne a gaban Mai Shari’a Sylvanus Oriji na babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Abuja tare da diyarsa, Fatima, da surkinsa, Jalal Sule Hamma, da wani kamfani mai suna Al Buraq Global Investment Limited.

Diya da surukin tsohon ministan ma sun musanta zargin aikata laifuka shida da ake tuhumar su da su lokacin da aka karanta musu a gaban mai shari’ar kotun.

Biyo bayan musanta tuhumar zamba da ake yiwa Hadi Sirika, diyarsa Fatima da ma surkin sa, lauyoyinsu sun gabatar da bukatar neman belinsu wanda mai shari’a Oriji ya amince da bukatar tasu aka bada belin su uku din a kan kudi naira miliyan 100 da kuma wadanda zasu tsaya masa guda biyu kowannensu.

Saidai an gindaya sharadi na bada belinsu kuma dole ne wadanda za su tsaya wa Sirika su kasance ’yan kasa da cikakken adireshi na gida kuma daya daga cikinsu ya mallaki kadara da asalin takardar shaidar mallaka daga ofishin Ministan birnin Abuja ya sanya wa hannu.

Haka kuma, kotun ya bayar da umarnin kada wadanda ake tuhuma su fita daga cikin Najeriya ba tare da izinin kotu ba kuma idan har ba zasu iya cika sharuddan belin ba, Mai shari’a Oriji ya ba da umarnin a tsare su a gidan yari har zuwa lokacin cika sharuddan belin.

Kotun ta dage zamanta kuma ta sanya ranar 10 ga watan Yuni domin fara shari’ar gadan-gadan.

Hadi Sirika tsohon ministan sufuri ne karkashin mulkin tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda ya shafe shekara 8 a kan karagar mulki.

Idan Ana iya tunawa, a ranar Larabar da ta gabata ne Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta ce za ta gurfanar da Sirika da wasu mutane uku a gaban kuliya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG