Jirgin da Najeriya ta gabatar a watan Mayu shatar shi aka yi daga kasar Ethiopia, Shugaban kamfanin jiragen saman Najeriya, Kyaftin Dapo Olumide ya fada a ranar Talata.
A ranar 26 ga watan Mayu jirgin na Nigeria Air ya baro Addis Ababa ya sauka a filin tashin jirage na Nnamdi Azikwe da ke Abuja kamar yadda rahotanni suka nuna.
Sai dai yayin da yake ba da bahasi a gaban kwamitin Majalisar Dattawan kasar, Kyaftin Olumodi, ya ce jim kadan bayan gabatar da jirgin, an mayar da shi kasar ta Ethiopia.
Tun a ranar da aka gabatar da jirgin, wasu kafofin yada labarai a Najeriya suka yi ta tsokaci kan cewa asalin jirgin na kasar Ethiopia ne.
Shugaban kwamitin na majalisar Dattawa, Sanata Biodun Olujimi, ya nuna takaicinsa kan yadda tsohon Ministan Sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya yi hanzarin gabatar da jirgin a rana ta karshe da Buhari zai kammala wa’adin mulkinsa.
A nasa bangaren, shugaban kwamitin kula da sufurin jirage a Majalisar Wakilai, Nnolim Nnaji, ya kwatanta lamarin a matsayin zamba cikin aminci.
Sai dai ma’aikatar sufurin jirgin saman Najeriya yayin mayar da martani, ta ce an gabatar da kamfanin ne ba wai an kaddamar da fara aikin jiragen ba ne.
A cewar Olumide, an yi haka ne don a tunatar da ‘yan Najeriya cewa aikin kaddamar da kamfanin yana nan ba a manta da shi ba.